Me ya sa aka fi kula da 'yan Chibok fiye da saura?

An dai samu wasu daga cikin 'yan matan sun tsira kamar Amina Ali
Bayanan hoto,

A watan Yunin 2014 ne dai aka yi garkuwa da 'yan matan da Chibok su fiye da 200 daga makarantar sakandare ta garin na Chibok

Masu sharhi, a Najeriya, sun fara tsokaci game da irin kulawar da ake bai wa 'yan matan Chibok da kungiyar Boko Haram ta mika wa gwamnatin Najeriya.

Da safiyar ranar Alhamis ne dai kungiyar ta Boko Haram ta saki 'yan matan Chibok guda 21, a wani mataki na fara tattauna da gwamnatin Najeriya.

Gwamnatin kuma ta dauki alhakin kula da karatun 'yan matan 21 tare da wata guda daya da 'yan kato da gora suka kwato a farkon wannan shekarar.

Sai dai wasu na ganin gwamnatin ta fi ba da fifiko wajen wadannan 'yan mata na Chibok fiye da sauran mata da kuma yaran da aka kwato daga hannun 'yan Boko Haram.

Dr. Hussaini Abdu, wanda shi ne shugaban Kungiya mai zaman kanta da ke Yaki da Talauci ta PLAN International a Najeriya, yana da irin wannan ra'ayi.

Ya ce yana mamakin yadda aka fi bai wa 'yan matan Chibok mahimmanci fiye da sauran mutanen da aka kwato daga hannun Boko Haram.

Dr. Hussaini ya ce yawancin mutanen da 'yan Boko Haram ke sakin su ana kai su sansanin 'yan gudun hijira ne, a jibge.

Ya kuma ce mutanen na fuskantar wariya da kyama daga 'yan uwansu da al'ummar gari saboda ana yi musu kallon wadanda suka zauna da 'yan Boko Haram.

Dr. Hussaini ya kara da cewa hali mafi muni ga wadannan mutane, shi ne idan mace ta samu ciki a hannun 'ya'yan kungiyar.

Ga yadda hirar Dr. Hussaini Audu ta kasance da Yusuf Ibrahim Yakasai.

Bayanan sauti

Chibok Boko Haram.