Ana ba wa 'yan matan Chibok fifiko fiye da sauran mutane.

Masana a Najeriya na ganin cewa gwamnatin kasar tana fifita 'yan matan Chibok da Boko Haram ta saki, a kan sauran mata da kananan yara da suka wahala a hannun kungiyar.