Shin Aminu Saira na da rai kuwa?

Saira ne mai ba da umarnin shirya fina-finan da ake ganin ya wuce sa'a

Asalin hoton, Instagram

Bayanan hoto,

Aminu Saira yana cikin koshin lafiya kuma tare da iyalansa

Fitaccen mai ba da umarni a shirya fina-finan Kannywood, Malam Aminu Saira, ya ce, yana nan da ransa kuma cikin koshin lafiya.

A makon da ya gabata ne dai aka yi ta watsa hotuna a kafar Sada Zumunta cewa Aminu Saira ya mutu sakamakon hadarin mota daga Kaduna zuwa Kano.

"Ni na fi wata guda ma rabona da zuwa Kaduna." in ji Saira.

"Abin da ya faru shi ne, yau kwana shida ke nan na dawo daga birnin Yamai, na zo gida na kwanta, sai iyayena da 'yan uwa suka yi ta kiran wayata cewa wai na mutu."

Daga nan ne kuma duniya ta dauka cewa Aminu Saira ya mutu.

Wannan jita-jitar dai ta sa jaruman fina-finan Hausa irin su Ali Nuhu suka yi ta amfani da kafafen sada zumunta wajen karyata batun.

Wannan dai ba shi ne karon farko da ake yada jia-jitar mutuwar jarumai da fitattun masu hada fina-finai ba.