Tabbas zan koma Juba — Riek Machar

An yi arangama tsakanin masu tsaron lafiyar Mista Machar da masu tsaron fadar shugaba Salva Kiir

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Riek Machar ya kasance tsohon mataimakin shugaba Salva Kiir

Tsohon mataimakin shugaban Sudan ta Kudu, Riek Machar wanda ya yi gudun hijra a watan Agusta, ya lashi takobin komawa kasar.

Da yake magana daga kasar Afirka ta Kudu, Mista Machar ya shaida wa BBC cewa kungiyarsa ta 'yan tawaye, za ta iya tattaunawa da bangaren Salva Kiir.

Kalaman nasa dai suna zuwa ne bayan gumurzun da aka yi a birnin Malakal, makon da ya gabata.

Yanzu haka dai mista Machar yana birnin Johannesburg ana duba lafiyarsa.

A watan Yuline masu tsaron lafiyar mista Machar suka yi arangama da sojoji masu tsare fadar shugaba, Salva Kiir, a inda aka kwashe kwanaki ana fafatawa.