Emirates zai takaita zurga-zurga a Afirka

Jiragen Emirates ba sa samun mai a kasashen Afirki

Asalin hoton, Google

Bayanan hoto,

Kamfanin Emirates ya ce rashin mai da matsin tattalin arziki ne zai kori kamfanin daga Afirka

Kamfanin jirgi na Emirates, ya ce zai takaita zurga-zurga a kasashen nahiyar Afirka ko kuma ma ya dakatar da jigilar zuwa wasu kasashen.

Kamfanin na Emirates, wanda ya sanar da daukar matakin a taron Kungiyar Masu Jiragen Sama ta Duniya a Dubai, ya ce hakan ya zama dole bisa la'akari da matsin tattalin arzikin da nahiyar Afirka take ciki.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya wanda ya rawaito labarin ya ce, shugaban kamfanin, Tim Clark, ya ce, jiragensu ba sa samun mai a kasashen Afirka.

Ya kara da cewa jiragen suna komawa kasashen turai ne domin shan man.

Tuni dai kamfanin ya rage jigilar zuwa biranen Lagos da Abuja na Najeriya daga biyu zuwa daya a kowace rana.