Zan ci gaba da fitowa a fina-finai - Ibrahim Mandawari

Ibrahim Mandawari na daga cikin jaga-jigan Kannywood

Asalin hoton, Mandawari

Bayanan hoto,

Ibrahim Mandawari ya gaji mahaifinsa Malam Muhammadu Shawai

An nada babban mai ruwa da tsaki a harkar fina-finan Hausa ta Kannywood, Ibrahim Muhammad Mandawari, a matsayin mai unguwar Mandawari, da ke cikin birnin Kano.

A ranar 7 ga watan Oktoba ne dai aka tabbatar da nadin a gaban hakimin Dala, sannan kuma mai martaba Sarkin Kano, Muhammad Sunusi na biyu ya amince da nadin.

Ya gaji mahaifinsa, Alhaji Muhammadu Auwalu Shawai, wanda Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na daya ya nada, a zamaninsa.

Asalin hoton, Ibahim Mandawari

Bayanan hoto,

Ibrahim Manawai ya durkusa gaban Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II yayin nada shi

Ibrahim Mandawari dai na daga cikin mutanen da suka assasa harkar fina-finan Hausa ta zamani a da ake kira Kannywood.

Ya shedawa BBC cewa zai ci gaba da shiryawa da kuma fitowa a fina-finan Hausa irin wadanda ya saba fitowa a baya.

'Yan uwa da abokan arziki dai sun taya shi murna bisa wannan nadin na sa.

Ya kuma shaidwa BBC cewa ya yi matukar farin ciki da wannan nadi da aka yi masa da ya gaji mahaifinsa.

Asalin hoton, Ibrahim Mandawari

Bayanan hoto,

Mandawari na daga cikin tsofaffin unguwanni a birnin Kano