An dage zabe a Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo

Al'ummar DRC da ke zanga-zanga.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Al'ummar DRC sun yi ta zazzafar zanga-zangar adawa da dakatar da zaben shugaban kasar

Jam'iyya da ke mulki a Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo ta kulla jarjejniyar da daya daga cikin jam'iyyun adawa domin dage zaben shugaban kasar har sai watan Afrilun 2018.

Ana shirin gudanar da zaben ne a watan Nuwamba, amma kuma jami'an zaben sun ce ana bukatar karin lokaci ne domin a yi rajistar masu zabe.

Shawarwarin na cikin wani bangare na wata yarjejeniya da ake shirin sanyawa hannu ranar Talata, bayan an kammala wata tattaunawar, da mafi yawan 'yan adawa suka kauracewa.

Hakan na zuwa ne bayan da kotun tsarin mulkin kasar ta amince da bukatar hukumar zaben kasar ta gabatar, na dakatar da zaben.

Wa'adin mulkin Shugaba Joseph Kabila na biyu zai kawo karshe a watan Disamba, kuma ana ta azalzalarsa da ya yi ya sauka daga kan mukamin.

A watan da ta gabata ma an yi zanga-zangar adawa da yunkurin dakatar da zaben, wacce ta yi sanadiyyar mutuwar akalla mutane 50.