Aisha Buhari ta tafi taro birnin Brussels

Matar Shugaban Nigeria Aisha Buhari

Asalin hoton, Aisha Buhari

Bayanan hoto,

Aisha Buhari ta yi tafiyar ne tare da 'yarta da kuma masu taimaka mata

Mai dakin shugaban Najeriya Hajiya Aisha Buhari, tana Brussels, babban birnin kasar Belgium, domin halartar wani taro kan al'amuran mata.

Aisha Buhari ta bayyana a shafinta na Twitter cewa za ta gabatar da jawabi a wajen bude taron kan "Gudunmuwar mata wajen samar da tsaro a duniya".

Wannan ne karon farko da matar ta shugaban na Najeriya ke fitowa bainar jama'a tun bayan hirar da ta yi da BBC Hausa, wacce ta janyo ce-ce-ku-ce.

Ta dai tafi Belgium ne bayan ta shafe kwanaki a wata ziyara da ta kai birnin London a makon jiya.

Kawo yanzu dai Hajiya Aisha Buhari ba ta ce komai game da zazzafar muhawarar da hirar ta haifar ba.

Haka kuma ba ta mayar da martani kan kalaman da mijinta, Shugaba Muhammadu Buhari, ya yi na cewa aikinta shi ne "dafa masa abinci da kuma kula da gidansa".

A cikin hirar, wacce ta ja hankalin duniya, Aisha ta zargi wasu 'yan tsirarun mutane da mamaye gwamnatin mijinta, inda ta ce suna hana ruwa gudu.

Sannan ta ce shugaban ya yi watsi da mafi yawan wadanda suka taimaka masa ya samu nasara a lokacin yakin neman zabe.

Asalin hoton, Aisha Buhari

Bayanan hoto,

Wannan ne karon farko da Aisha Buhari ke fitowa bainar jama'a tun bayan hirarta da BBC

Asalin hoton, Aisha Buhari

Bayanan hoto,

Ta jirgin kasa Hajiya Aisha Buhari ta tafi Brussels daga London