'Ba za a yi maraba da Machar a Juba ba'

Riek Machar da Salva Kiir

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Riek Machar da Salva Kiir sun zama abokan gaba bayan yakin 'yanto kasarsu daga Sudan

Kakakin shugaban Sudan ta Kudu ya shaida wa BBC cewa bai dace ba jagoran 'yan tawaye, Riek Machar, ya koma babban birnin kasar Juba ba, duk da cewa ba za a kama shi ba.

Mista Ateny Wek, ya ce a yanzu Riek Machar, ba shi da sauran wata rawa da zai taka a matsayin jagoran siyasa a kasar.

Tun farko a wata hira da BBC, Mr Machar wanda aka nada mataimakin shugaban kasa Salva Kiir, a wata yarjejeniyar zaman lafiya, kuma ya tsere daga Sudan ta Kudu, bayan mummunan fada a Juba a watan Yuli, ya ce zai koma kasar.

Amma kuma an ji yo Kakakin shugaba Salva Kiir, yana cewa bai kamata Mr Machar, ya ma yi tunanin koma wa kasar ba, kafin zabukan 2018.

Riek Machar na son komawa gida Sudan ta Kudu, ko dai domin ya cigaba da yakin da yake yi da abokin gabarsa, Shugaba Salva Kiir, ko kuma ya yi aiki da shi idan har za a cimma yarjejeniyar yin hakan.

Bayan da aka tilasta wa Mista Machar tserewa daga babban birnin kasar, Juba ne, aka cire shi daga mukamin mataimakin shugaban kasa.

Rikicin na Sudan ta Kudu dai ya raba mutane sama da miliyan biyu da rabi da gidajensu, tun lokacin da aka fara shi a watan Disamba na shekara ta 2013.