Za a rika dandake masu yi wa yara fyade a Indonesia

Shugaba Joko Widodo na Indonesia

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Shugaba Widodo ya ce babu wani sassauci kan masu laifin fyade

Shugaba Joko Widodo na Indonesia ya ce sabuwar dokar yin amfani da guba wajen yi wa duk wanda aka samu da laifin cin zarafin yara ta hanyar lalata dandaka, za ta rage yawan laifuka a kasar.

Shugaba Widodo ya gaya wa BBC cewa Indonesia na mutunta hakkin dan adam da kundin tsarin mulki, amma fa idan aka zo kan batun laifin da ya shafi cin zarafi, gwamnati za ta dauki hukuncin ba sani ba sabo.

A farkon wannan watan nan ne, kasar ta yi dokar hukunta wadanda aka samu da laifin yi wa yara fyade taure (fidiya), ta hanyar amfani da guba, bayan gungun wasu bata-gari sun yi wa wata yarinya 'yar shekara 14 fyade daga bisani kuma suka kashe ta.

Kungiyar likitocin kasar ta Indonesia ta ce mambobinta ba za su shiga aiwatar da dokar ba domin ta saba ka'idojin aikin likita.