Nigeria: Kayan hadin burodi sun yi tsada

Gasasshen Burodi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Farashin fulawa da madara da sauran kayan hada burodi sun yi tashin da aka dade ba a gani ba.

A Najeriya masu gidajen burodi na kokawa da tsadar kayan da ake yin burodin da suka hada da sukari da fulawa da madara da sauransu, kuma hakan na barazana ga sana'ar tasu..

Masu wannan sana'a na cewa a yanzu dole ta sa suke rage yawan burodin da suke yi, da rage ma'aikata, kuma ba su da zabi illa kara farashin burodi.

Sannan kuma sun ce, suna fargabar idan aka ci gaba da tafiya a haka, za a wayi gari burodi ya yi karanci ko ma sun dakatar da yinsa.

Wani mai gidan burodi a Kaduna da ke arewacin kasar, ya ce matukar aka ci gaba da tafiya a yanayin da ake ciki to kuwa za a wayi gari babu burodi a kasar.

A ranar Laraba ne dai kungiyar masu burodi ta jahar Lagos za ta bayyana karin farashinsa.

Farashin kayan masarufi sun yi tashin gwauron zabbi a Najeriya, inda 'yan kasar ke kokawa da tsadar kayan bukatun yau da kullum.