Mutane na tserewa daga Mosul

Kiyasi ya nuna akwai 'yan IS guda 5,000 a rabe a birnin na Mosul
Bayanan hoto,

Daruruwan mutane na guduwa daga Mosul, yayin da dakarun sojin Iraqi suke karato birnin

Wata tawagar fararen hula su 900, ta tsere daga birnin Mosul, a dai-dai lokacin ake cigaba da fafatawa domin kwato birnin daga hannun kungiyar IS.

Wannan dai shi ne karon farko da gungun mutane masu yawa suka fice daga birnin tun lokacin da gwamnatin kasar ta fara luguden wuta a kan 'yan IS, ranar Litinin.

Ana dai tsammanin cewa akwai mutane kusan miliyan 1.5 a Mosul sannan kuma akwai mayakan IS guda 5,000, ɓoye a birnin.

Akwai tsoron cewa mayakan na IS ka iya shiga cikin mutane domin kare kansu daga dakarun kasar Iraqi.