Emirates zai dakatar da jigilar Dubai zuwa Abuja

Jiragen Emirates ba sa samun mai a kasashen Afirki

Asalin hoton, Google

Bayanan hoto,

Kamfanin Emirates ya ce rashin mai da matsin tattalin arziki ne zai kori kamfanin daga Afirka

Kamfanin jiragen sama na Emirate Airline, ya sanar cewa zai daina jigila tsakanin birnin Dubai da ke Hadaddiyar Daular Larabawa, da babban birnin Najeriya, Abuja.

Kamfanin dai yana yin zurga-zurga sau hudu a duk mako, daga Dubai zuwa Abuja.

Yanzu haka, kamfanin ya ce daga ranar 30 ga watan Oktoba, zai dakatar da jigilar tsakanin biranen biyu.

Mai magana da yawun kamfanin ya ce jiragen na Emirates za su rinka yin jigila ne daga Dubai zuwa birnin Legas a Najeriya.

Kamfanin ya ce dakatar da jirgin nasa daga zuwa Abuja zai ba su damar karkata akalar jiragen zuwa inda za a rinka samun riba sosai.

Ana dai ganin wannan matakin zai kawo babban koma baya ga tattalin arzikin kasar wanda tuni yake fuskantar komada.

Dubai dai ta kasance daya daga cikin biranan da 'yan kasuwar Najeriya da ma masu son shakatawa suke yawan zuwa.

Daman dai a ranar Talata kamfanin ya sanar da takaita zurga-zurga a nahiyar Afirka saboda matsalar man jirgi da kuma ta tattalin arzikin da kasashen ke ciki.