'Jiga-jigan IS sun gudu daga Mosul'

Mayakan Iraki

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Dakarun Iraki sun durfafi Mosul domin karon-batta da mayakan IS

Hukumomin sojin kasa na Amurka sun ce akwai alamun da ke nuna jagororin kungiyar IS, sun gudu daga Mosul, yayin da dakarun Iraki da kawayensu suka durfafi birnin.

Janar Gary Volesky, na sojin Amurkan, ya ce, dakarunsa sun ga alamun da suka nuna cewa mayakan kungiyar na ficewa daga birnin.

Amma kuma ya ce yana ganin mayakan kungiyar da dama 'yan kasashen waje za su ja daga saboda zai yi wuya su iya sulalewa su gudu, kamar takwarorinsu 'yan Iraki.

Janar din ya ce kafin a samu nasarar kwato birnin na Mosul lalle sai an yi dauki-ba-dadi, amma kuma dakarun Iraki a shirye suke da hakan.