'Yan matan Chibok sun fi son zama da 'yan Boko Haram'

'Yan matan Chibok

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Wasu na ganin 'yan Boko Haram sun juya tunanin wasu daga cikin 'yan matan na Chibok

Wasu rahotannin na cewa fiye da 'yan matan Chibok 100 daya da ke hannun 'yan Boko Haram sun fi son zama a hannun mayakan maimakon dawowa wurin iyayensu.

Shugaban kungiyar cigaban al'ummar Chibok, Mr Pogba Bitrus, wanda ya bayyana hakan ga kamfanin dillancin labarai na AP, ya ce yana ganin 'yan Boko Haram sun sauya tunanin 'ya'yan nasu ne.

Ko kuma a cewarsa, 'yan matan suna jin kunyar dawowa gida saboda gudun yadda jama'a za su rika kallonsu, ko kuma su fuskanci tsangwama.

Rahotannin sun bayyana ne a yayin da shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya sha alwashin kara zage damtse wajen ganin an sako karin 'yan matan 83.

A makon da ya gabata ne bisa wata yarjejeniya da kungiyar agaji ta Red Cross da gwamnatin Switzerland suka shiga tsakani, aka sako 21 daga cikin 'yan matan bayan shafe fiye da shekara biyu.

A watan Afrilun 2014 ne dai Boko Haram ta sace 'yan matan sama da 200, a makarantarsu da ke garin Chibok, na jihar Borno, a lokacin da suke jarrabawa, lamarin da ya ja hankalin duniya.

Kuma a ranar Lahadi ne suka gana da iyayensu cikin annashuwa, a karon farko tun bayan sace su.

Asalin hoton, Nigeria Government

Bayanan hoto,

A ranar Laraba ne Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da 'yan matan da aka sako

Asalin hoton, Nigeria Government

Bayanan hoto,

Wasu daga cikin 'yan matan sun haihu bayan da aka yi musu auren dole