Pakistan ta hana sa fim din India a talabijin da rediyo

Wasu daga cikin taurarin Bollywood

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Fina-finan India suna da farin jini a Pakistan

Pakistan ta hana sanya duk wani shiri ko fim na India a tashoshin talabijin da na rediyo da ke kasar daga ranar Juma'a.

Hukumar kula da gidajen rediyo da talabijin ta Pakistan ta ce duk wata tasha d ta saba wa dokar za ta rasa lasisinta sannan kuma za a gurfanar da masu ita a kotu.

Dangantaka tsakanin India da Pakistan ta yi tsami a kwanan nan, inda kasashen biyu suka rika hana sanya fina-finan juna a tashoshin talabijin da ke kasashen amma ba a hukumance ba.

A ranar Talata ne wani darektan fim na Indiya, Karan Kohar, ya yi alkawarin daina sanya 'yan fim na Pakistan a fina-finansa, bayan da wata kungiyar masu ra'ayin rikau a India ta sha alwashin kai hari kan gidajen sinimar da ke nuna sabon fim dinsa, wanda akwai wani tauraron fim dan Pakistan, Fawad Khan a cikinsa.