Kungiyar lauyoyi na so a dakatar da alkalan Nigeria

Wasu lauyoyin Najeriya

Asalin hoton, EFCC

Bayanan hoto,

Batun kama alkalan na ci gaba da janyo cece-kuce a tsakanin 'yan Najeriya

Kungiyar lauyoyi ta Najeriya ta yi kira a dakatar da alkalan da ake zargi da cin hanci a kasar.

Shugaban kungiyar, Mahmoud Abubakar (SAN), ya ce dole ne hukumar da ke sa ido kan shari'ar kasar, NJC, ta dakatar da alkalan da aka kama bisa zargin cin hanci idan tana so kimarsu ta dawo a idanun 'yan Najeriya.

Ya yi wannan kira ne a wajen bikin girmamawa ga Mai shari'a Sotonye Denton-West ,daya daga cikin alkalan daukaka kara da ke Abuja, wacce ta yi ritaya.

Mahmoud Abubakar ya kara da cewa, "Ya kamata NJC ta dauki matakan gaggawa na kare martabar fannin shari'a da kotuna. Don haka muna kira da babbar murya a yi wa wadannan alkalai ritayar dole har sai an kammala shari'ar da ake yi musu.''

Tun da farko dai kungiyar lauyoyin ta caccaki hukumar tsaro ta farin kaya, DSS saboda dirar mikiyar da ta yi a gidajen alkalai a sassan kasar daban-daban, inda ta kama su.

DSS ta kaddamar da samamen ne a babban birnin kasar, Abuja da Port Harcourt da Gombe da Kano da Enugu da kuma Sokoto, inda ta kama alkalan guda bakwai, wadanda ta samu makudan kudade a gidajensu.

Alkalan sun hada da Sylvanus Ngwuta da Inyang Okoro na kotun koli, da kuma Muazu Pindiga da Adeniyi Ademola na manyan kotu.

Haka kuma an kori babban alkakin kotun jihar Kano, mai shari'a Kabiru Auta da babban alkalin kotun daukaka kara da ke zama a Ilorin, mai shari'a Mohammed Ladan Tsamiya da kuma babban alkalin kotun Enugu, mai shari'a I. A. Umezulike bisa zargin karbar hanci.