An tsare mutane 1,600 a Habasha

Masu zanga-zangar kin jinin gwamnati a Habasha

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Masu zanga-zangar kin jinin gwamnati a Habasha

Hukumomi a kasar Habasha sun tsare mutane 1,600 a kokarin su na karfafa matakan tsaro karkashin dokar ta baci da aka kafa.

Wadannan mutanen da aka kama baya ga mutane 1,000 ne da aka tsare tun ranar Litini kusa da babban birnin kasar.

Kafar yada labarai ta FBC ta ambato wata sanarwar gwamnati na cewa an tsare mutanen ne a yankin Oromia da kuma Amhara wuraren da aka fuskanci mummunar zanga-zanga.

An dai sanya dokar ta baci na watanni shida ne sakamakon zanga-zangar kin jinin gwamnati.

A karkashin dokar dai za'a iya tsare mutane ba tare da takardar sammaci ba har na tsawon wa'adin dokar.

Kafar labarai ta FBC ta kara da cewa wadanda aka kama ana zargin su ne da hannu a tashin hankali na baya bayan daya barke inda ta ce an yi nasarar karbe makamai da dama.

Kawo yanzu dai ba'a bayyana wurin da ake tsare da mutanen ba.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Wannan shi ne rikici mafi muni da kasar Habasha ta taba fuskanta cikin shekaru da dama

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

An shafe watanni ana fuskantar mummunar zanga zanga a Habasha

Sai dai wasu kungiyoyi kare hakkin da Adam sun ce akalla mutane 500 ne suka mutu sakamakon arangama da jami'an tsaro a cikin watanni goma sha daya da aka kwashe ana zanga-zangar kin jin gwamnati.

A makon daya gabata ne Firai Minista Hailemariam Desalegn ya ce adadin mutanen da suka mutu ba su kai haka ba.

Masu zanga zangar dai suna abkawa gine-ginen kasuwanci wadanda ba na gwamnati ba da kuma wasu gine gine mallakar 'yan kasashen waje.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Kasar Habasha

An dai fara zanga-zangar daga Oramia ne a watan Nuwamba inda mutane suka fito domin nuna adawa da shirin fadada babban birnin Addis Ababa zuwa yankin su.

Duk da cewa gwamnati ta dakatar da yunkurin hakan amma an ci gaba da yin zanga zanga.

An kuma gudanar da zanga-zanga a yankin Amhara da ke kasar.

A ranar 9 ga watan Oktoba ne dai aka kafa dokar ta baci mako guda bayan da mutane 55 suka hallaka a wani turmutsisi lokacin bukin ibada a yankin Oroma wanda ya rikide ya koma tarzoma.

Masu fufutika dai sun zargi jami'an tsaron gwamnati da haddasa fargaba sai dai gwamnati ta ce masu zanga- zanga da ke cikin taron bukin ibadar ba su da mutunci.