Direbobin bas na yajin aiki a Kano

Hukumomi sun umurci duk wani direban bas na haya a Kano da ya yi fenti

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Hukumomi sun umurci duk wani direban bas na haya a Kano da ya yi fenti

Direbobin bas-bas a jihar Kano dake arewa maso yammacin Nigeria sun fara wani yajin aiki na sai abin da hali ya yi.

Direbobin dai na zargin jami'an 'yan sanda dana hukumar da ke kula da zirga-zirgar ababen hawa a jihar wato KAROTA da kuntata musu.

A cewar su, jami'an KAROTA suna tilastawa kowane direban bas yin fenti inda ake cin tarar duk wani direban da bai yi fenti ba.

Sun kuma yi ikirarin cewa jami'an KAROTA na daukar wannan mataki ne ba tare da sun ba direbobin wa'adi na yin fenti ba.

Sai dai a nasu bangaren hukumomin sun musanta cewa basu ba direbobin wa'adin yin fenti na motocin su ba.