Za a kafa hukumar arewa maso gabashin Najeriya

Majalisar dokokin Nigeria
Bayanan hoto,

Majalisar dokokin Nigeria

Majalisar dattawan Nigeria ta amince da kudurin dokar kafa hukumar kula da yankin arewa maso gabashin kasar.

Majalisar ta amince da kudurin dokar ne bayan ta yi mata karatu na uku.

Dokar dai ta tanadi bada kulawa ta musamman ga yankin na arewa maso gabas, wanda yaki ya yi wa mummunar illa.

To sai dai baya ga jihohin na arewa maso gabas, majalisar ta amince a shigar da karin wasu jihohin Kano da kuma Pilato karkashin kulawar hukumar.