Ana taron koli a kan Zika a kasar Cuba

Ana danganta cutar Zika da cizon Sauro
Bayanan hoto,

Ana danganta cutar Zika da cizon Sauro

Kwararru a kan kiwon lafiya daga Amurka da kasashen Latin Amurka da Karebiyan fiye da talatin, suna yin taron kolinsu na farko a kan yadda za a tunkari cutar Zika.

Masana kimiyya da Kungiyar lafiya ta Duniya suna ganin sauron da ke dauke da cutar ne ake alakantawa da cutar da haddasa haihuwar gilu.

Kasar Cuba ce mai masaukin taron, wadda ta sami nasarar dakile bazuwar cutar ta Zika a kasarta