Kalaman Trump na da hadari da dimokradiyya —Obama

Barack Obama

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Trump dai na bayan Hillary a wajen farin jini

Shugaba Barack Obama na Amurka ya ce nacewar da dan takarar jam'iyyar Republican ya yi cewa mai yiwuwa ba zai amince da sakamakon zaben shugaban kasar da za a yi ba na da hadari.

Da yake jawabi a wajen gangamin yakin neman zaben 'yar takarar jam'iyyar Demokrat Hillary Clinton a Miami, shugaban ya ce kalaman na Donald Trump na zagon kasa ga tsarin dimokradiyyar Amurka.

Mr. Trump dai ya ki ya ce zai amince da sakamakon zaben wanda za a yi ranar 8 ga watan Nuwamba a yayin wata muhawara da aka nuna kai tsaye ta akwatunan tallabijin.

Bugu da kari kuma a yayin wani gangamin yakin neman zabensa a jihar Ohio ranar Alhamis, dan takarar na jam'iyyar Republican ya ce zai amince da sakamakon ne kawai idan shi ne ya ci.