Atletico Madrid ba za ta sayi sabon dan wasa ba

An amince kungiyoyin su dauki 'yan wasa a yayin da suke ci gaba da daukaka kara

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

An amince kungiyoyin su dauki 'yan wasa a yayin da suke ci gaba da daukaka kara

Atletico Madrid ba za ta samu damar sayen sababbin 'yan wasa a watan Janairu ba a yayin da kungiyar ke ci gaba da haramcin da Fifa ta yi musu.

A watan Janairun da ya wuce ne Fifa ta haramta wa kungiyar da kuma takwararta Real Madrid sayen sababbin 'yan wasa tsawon shekara biyu saboda keta dokar sayen 'yan wasan da ba su kai shekara 18 ba.

Sai dai an amince wa kungiyoyin su dauki 'yan wasa a yayin da suke ci gaba da daukaka kara kan hukuncin na Fifa.

Amma yanzu Atletico ta amince ta "sarayar da damarta ta neman a dakatar da haramcin da aka yi mata har sai bayan hunturu".

An kyale Real ta sayi 'yan wasa a Janairu.

An taba yanke irin wannan hukuncin kan Barcelona a watan Afrilun shekarar 2014 kuma an hana su sayen 'yan wasa a shekarar 2015 bayan sun kasa yin nasara a karar da suka daukaka.