Shugaba Buhari ya dauki mata da daraja -Minista

Kristine Legarde da Kemi Adeosun

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Akwai dai mata masu rike da manyan mukamai a gwamnatin Buhari

Ministar kudi ta Najeriya Kemi Adeosun ta ce kallon da wasu ke yi wa shugaban kasar na wanda bai dauki mata da daraja ba kuskure ne.

Shugaba Muhammadu Buhari dai ya fuskaci suka daga mutane a sassa daban-daban na duniya bayan kalamin da ya yi a kwanan baya cewa aikin matarsa shi ne dafa abinci da kula da turakarsa; abin da ya sa wasu ke yi masa kallon wanda bai dauki mata da daraja ba.

Amma a wata hira da BBC Mrs. Adeosun ta ce ta yin la'akari da yadda shugaban ya nada mata a manyan mukamai a gwamnatinsa za a fahimci yadda ya dauki mata(da daraja).

''Ina aiki da shi kut-da-kut kuma ban taba ganin ya nuna kaskanci ga mata ba, a ganina ya ma fi bai wa mata fifiko.'' In ji ministar kudin.