An yi watsi da bukatar Rasha na sa ido a babban zaben Amurka da za a yi

A ranar 8 ga watan Nuwamba 2016 ne za a gudanar da babban zabe a Amurka

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

A ranar 8 ga watan Nuwamba 2016 ne za a gudanar da babban zabe a Amurka

Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta yi watsi da bukatar Rasha na sa ido a babban zaben da za a yi a kasar a jihohi guda uku.

A cikin wasu wasiku da ya aike zuwa jihohin Oklahoma da Texas da kuma Louisiana, jakadan Rasha a Amurka ya bukaci a basu dama a hukumance ta kasancewa a wasu rumfunan zabe domin suyi nazari akan yadda Amurka ke gudanar da zabe.

Dukkan jihohi ukun sun ki amince da bukatar Rashan.

Jihar Oklahoma ta ce dokar jihar ta hana wani da ba jami'in zabe ba ko kuma mai jefa kuri'a ya kasance a rumfar zabe a lokacin da ake jefa kuri'a.