An ci tarar tsohon dan wasan Chelsea Didier Drogba

Didier Drogba ya lashe kofin Premier da na zakarun turai guda hudu da Chelsea

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Drogba ya lashe kofin Premier da na zakarun turai guda hudu da Chelsea

An ci tarar tsohon dan wasan Chelsea Didier Drogba saboda ya ki bugawa Montreal Impact wasa a makon jiya.

Drogba, mai shekara 38, bai buga wasan da kungiyarsa ta yi da Toronto ba, kuma bayan an gama wasa ne koci Mauro Biello ya ce dan wasan "bai amince a sanya shi a benci ba".

Hakan dai ya sa an ci tarar Drogba kudin da ba a fadi adadinsu ba saboda rashin buga wasan.

Kungiyar Montreal, wacce ke ta biyar a gasar the Eastern Conference, za ta fafata da New England Revolution ranar Lahadi.

Drogba, wanda ya bar Chelsea a watan Yulin shekarar 2015, ya buga wa Impact wasanni biyu ne kawai cikin wasanni hudun da suka yi.

Dan wasan ya zura kwallaye 10 a fitowa 21 da ya yi a kakar wasa ta bana.