An haramta shan giya a kasar Iraqi

Ana sayar da giya a kananan kantunan birnin Bagadaza

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Ana sayar da giya a kananan kantunan birnin Bagadaza

Majalisar dokokin Iraqi ta amince a haramta yin giya da sayar da ita da kuma shigar da ita kasar.

Masu goyon bayan kudirin dokar sun bayar da hujjar cewa kundin tsarin mulkin kasar ya haramta duk wani abu da ya yi sabani da dokokin Musulinci, ciki har da shan giya.

Sai dai masu hamayya sun ce matakin ya sabawa kundin tsarin mulkin, wanda ya amince kowanne mutum ya yi addinin da yake so.

Sun kara da cewa za su kai batun gaban kotu domin yanke hukunci.

Wani jami'in gwamnatin kasar ya shaida wa kamfanin dillancin labaran AFP an sanya batun haramta shan giyar ne a cikin kudirin dokar sauye-sauye kan dokokin tafiyar da mulkin biranen kasar.

Lamarin dai na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ke yunkurin kwato birnin Mosul daga mayakan kungiyar IS.