An harbe wani janar na sojin Masar

Egypt Soldiers
Bayanan hoto,

Sojojin Masar

An harbe wani janar din sojan kasar Masar har lahira, wanda yayi aiki a yankin Sinai.

An harbe Birgediya Janar Adel Ragaei ne a kusa da gidansa a Alkahira.

Janar Ragaei ya ta ba zama kwamandan sashin kula da makaman yaki dake yankin Sinai, inda dakarun Masar ke yaki da mayaka masu da'awar jihadi dake ikirarin goyon bayan IS.

Daruruwan sojoji da 'yan sanda ne aka kashe a yankin, kuma mayaka masu kishin Islama suka kai hare-hare a kusa da Alkahira.

Sai dai ba kasafai ake kashe manyan jami'an tsaro ba.