Kotu ta yankewa Morsi daurin shekaru 20

Mohammed Morsi

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Tsohon shugaban Masar Mohammed Morsi

An yanke wa tsohon shugaban kasar Masar, Mohammed Morsi, hukunci na karshe, a jerin shari'o'i da yake fuskanta a kasar.

Kotun daukaka kara a kasar ta yankewa tsohon shugaban wanda aka hambarar daurin shekara ashirin a gidan yari, saboda hannu da yake da shi a mummunar tarzoma a wajen fadar shugaban kasar a 2013.

Yunkurin Mista Morsi a wancan lokaci na karawa gwamnatinsa iko, ya haifar da zanga-zanga, kuma amfani da karfi sosai wajen dakili zanga-zangar ya sa sojoji kwace mulkin kasar.

Har yanzu dai lauyoyinsa na daukaka kara game da hukuncin daurin rai-da rai da aka yanke masa saboda tserewa daga gidan kaso a 2011, da kuma sa'insa da 'yan sansa a 2011 lokacin da aka hambarar da shugaba Hosni Mubarak.