An cigaba da gwabza fada da kuma hare-hare ta sama a Aleppo

An cigaba da kai hare-hare ta sama a Aleppo
A Syria an cigaba da gwabzawa da kuma kai hare-hare ta sama a birnin Aleppo bayan kawo karshen yarjejeniyar tsagaita wutar da Rasha ta ayyana ba tare da wata yarjejeniya ba.
Anyi artabu da kuma harba makaman artilari a wurare daban-daban a kusa da inda aka ja daga ciki har da unguwannin Sheikh Saeed da Salah el-Deen.
Rahotanni sun ce an kai hare-hare ta sama kan wasu yankunan da 'yan tawaye ke rike da su, ko da yake har yanzu ba a tantance ko jiragen da ke kai hare-haren ba.
Majalisar dinkin duniya ta ce ba ta samu damar kwashe kowa daga wuraren da aka yiwa kawanya ba a lokacin da yarjejeniyar tsagaita wutar ke aiki saboda tunanin ba bu tabbas wajen kare jami'anta daga wata masifa.