'Yan fashin teku sun sako mutum 26 a Somalia

Dan fashin teku

Asalin hoton, Mohammed Dahir

Bayanan hoto,

An sako mutanen bayan kwashe watanni 18 ana tattaunawa

Masu shiga tsakani na kasa da kasa sun ce 'yan fashin teku a Somaliya sun sako wasu maza 26 da suka yi garkuwa da su tun shekaru biyar din da suka gabata.

Sun kama jirgin ruwan da suke tafiya a ciki, kirar FV Naham 3 ne, a kudu da tsibirin Seychelles a wata Maris na shekara ta 2012.

An tsare mutanen da jirgin nasu daura da gabar tekun Somaliya har sai da ya nutse sannan aka zo da su kan tudu kana aka ci gaba da tsare su a wani kurmi.

Mutanen dai sun fito ne daga kasashen Cambodia, da China, da Taiwan, da Indonesia, da Philippines, da kuma Vietnam; amma jirgin na kasar Oman ne.