A tsawaita yarjejeniya tsagaita wuta a Yemen -MDD

Zanga-zangar kin-jinin-gwamnati a Sanaa

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

A watan Maris na shekara ta 2015, kasar Sa'udiyya da kawayenta a yankin mashigin tekun fasha suka kaddamar hare-hare da jiragen sama kan 'yan tawayen.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga bangarorin da ke fada da juna a Yemen da su kara tsawaita wa'adin yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma ta tsawon wasu kwanaki uku.

Tsagaita wutar ta sa'o'i 72 dai ta kare ne da karfe 11 da Minti 59 na daren Assabar agogon kasar kuma kawo yanzu babu wata magana daga kowane bangare kan ko mayakan za su amince a tsawaita tsagaita wutar.

Manzon musamman na majalisar zuwa kasar ta Yemen, Ismail Ould Cheikh Ahmed, ya ce yarjejeniyar ta bai wa ma'aikatan majalisar damar kai agajin abinci da sauran abubuwan bukatar rayuwa zuwa yankuna daban-daban da a baya ba iya shigar su.

Ya bayyana fatan cewa idan bangarorin da ke fada da juna suka amince aka kara tsawaita wannan yarjejeniya, hakan zai iya kai ga samo bakin zaren warware rikicin gaba daya.

Fadan na Yemen dai ya soma ne a shekara ta 2014 lokacin 'yan tawayen Houthi mabiya akidar shi'a da ke da mazauni a arewacin kasar suka kwace iko da babban birnin kasar Sana'a kuma daga bisani suka mamaye mafi yawancin kasar.