'Ramalan Yero ya kashe N2.1bn a kan sayen alewa'

Yero bai yi raddi ba
Bayanan hoto,

Yero bai yi raddi ba

Gwamnatin jihar Kaduna da ke Najeriya ta yi zargin cewa gwamnatin da ta gada ta kashe N2.1bn wajen sayen alewa da sauran kayan kwalam-da-makulashe a shekara daya kacal.

Kwamishinan kasafin kudi na jihar Mohammed Abdullahi ne ya bayyana hakan a karshen makon jiya.

A cewarsa, gwamnatin Mukatar Ramalan Yero ta kashe kudin ne a shekarar 2014, yana mai cewa ta kuma kashe N2bn domin bayar da horo ga ma'aikatan da ba sa bukatar horo a wancan lokacin.

Ya kara da cewa, ga misali, gwamnatin Yero ta bai wa mai kididdigar kudi horon da jami'in da ke zayyana gidaje ne ke bukata.

Mohammed Abdullahi ya ce gwamnatin Yero ta kashe N40m a duk wata wajen sayen soyayyun kaji da shinkafar da ake ci a gidan gwamnatin jihar.