"Mun riƙa cin ɓeraye don mu rayu"

Matuka jirgin ruwa

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

An kwaso matuka jirgin ruwa zuwa Kenya bayan da aka sako su

Wasu daga cikin matuƙa jirgin ruwan nan da 'yan fashi a tekun Somaliya suka sako su bayan sun shafe kusan shekaru biyar ana garkuwa da su sun riƙa cin ɓeraye domin su rayu.

Daya daga cikin matuƙa jirgin ruwan dan kasar Filipino Arnel Balbero ya ƙara da cewa an riƙa ba su ruwa kaɗan kaɗan a lokacin da ake garkuwa da su.

An dai kame mutanen su 26 lokacin da su ke cikin jirgin su a shekarar 2012 inda aka kai su kasar Somaliya.

A ranar Asabar ne aka sako mutanen bayan da aka biya kuɗin fansa.

Mutuƙa jirgin sun fito ne daga kasashen China da Philippines da Cambodia.

Saura sun haɗa da Indonesia da Vietnam da kuma ƙasar Taiwan.

Mr Balbero yana ɗaya daga cikin matuka jirgin ruwa mai suna FV Naham 3 a lokacin da masu fashi a teku 'yan kasar Somaliya suka kame su a yammacin Seychelles.

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Tun da farko mutane 29 aka yi garkuwa da su sai dai mutum daya ya mutu lokacin da aka kame su inda biyu suka mutu saboda rashin lafiya

Wata ƙungiya mai kanta Oceans Beyond Piracy ta ce an kashe mutum ɗaya daga cikin matukan a lokacin da aka cafke su.

Sai dai shekara guda bayan da aka garkuwa da su jirgin ya nutse inda aka maido da mutanen zuwa kan tudu a Somaliya.

Daga bisani kuma wasu mutaka biyu sun mutu sakamakon rashin lafiya.

Mr Balbero ya shaida wa BBC cewa sun sha uƙuba shekaru huɗu da rabi da suka kwashe ana garkuwa da su.

Da aka tambaye shi yadda masu fashin suka riƙa kula da su sai ya ce, "suna ba mu ruwa kadan, mun riƙa dafa ɓeraye muna ci a cikin jeji don mu rayu."

Ya ƙara da cewa " idan mu ka ji yunwa muna cin komai muka gani."

Bayanan hoto,

Hotunan da aka fitar a 2014 sun nuna mutanen a ƙanjame

Ana kyautata zaton cewa mutanen da aka sako su ne na ƙarshe da masu fashi a teku 'yan ƙasar Somaliya ke garkuwa da su tun bayan da a ka fuskanci ƙaruwar fashi a teku a tsakiyar shekarar 2000.

An dai samu raguwar barazanar da ake fuskanta daga masu fashi a gabar tekun Somalia a 'yan shekaru nan saboda sintiri na jami'an sojin ruwa na ƙasa da ƙasa da ake yi a tekun.

An kuma samu wasu hoton na matuƙa jirgin ruwan da suka rayu wadanda masu fashin a tekun suka dauka a 2014 yayin da ake tattauna wa inda aka buƙaci shaidar da za ta nuna cewa suna raye.

Hotunan da wani dan Majalisar dokoki na ƙasar Taiwan ya fitar wanda kuma ya ke cikin masu tattauna sun nuna mutanen a ƙanjame, inda wasu dauke mutane suka zagaye su da bindigogi fuskokin su a rufe.

Kafafen yada labarai a kasar Taiwan sun ce ma'aikatar harkokin wajen ƙasar ta ce an sako mutanen ne bayan da masu jirgin ruwa suka biya kuɗin fansa.