An yi harbe-harbe a birnin Bangui

'Yan adawa sun yi kira ga jama'a da kada su fita aiki

Asalin hoton, FRED DUFOUR

Bayanan hoto,

'Yan adawa sun yi kira ga jama'a da kada su fita aiki

Rahotanni daga Bangui babban birnin Jamhuriyar tsakiyar Afirka sun ce an yi harbe-harbe a tsakiyar birnin da safiyar ranar Litinin.

Ana dai kallon lamarin a matsayin tauna tsakuwa domin aya ta ji tsoro.

'Yan adawa sun yi kira ga jama'a da kada su fita aiki har sai dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya sun fice daga kasar.

Wasu 'yan kasar dai na zargin dakarun majalisar da rashin daukar mataki don dakatar da kashe jama'ar da ba sa dauke da makamai.

To sai dai gwamnati ta bukaci jama'a da su yi watsi da wannan kira su fita don gudanar da harkokinsu tare da bayar da tabbacin tsaron lafiyarsu.