Nigeria: Dangote ya kori ma'aikata 48

Alhaji Aliko Dangote

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

An yi kiyasin cewa Aliko Dangote shi ya fi kowa arziki a Afirka

Kamfanin Dangote ya kori wasu ma'aikatansa 48 saboda matsalar tabarbarewar tattalin arziki da ake fama da ita a Nigeria.

Ma'aikatan da aka kora sun hada da 36 'yan kasashen waje da kuma 'yan Nigeria 12 ne.

Rahotanni sun ce korar ma'aikatan bai rasa nasaba da tsadar farashin kayayyaki a Nigeria musamman karancin kudaden waje da ake fuskanta.

Bayan gwamnatin kasar dai kamfanin Dangote na sahun gaba wajen yawan ma'ikata a Nigeria.

Watanni biyu da suka gabata ne kafar watsa labarai ta Bloomberg ta ruwaito cewa a 2016, kamfanin Dangote ya tafka asarar dala biliyan 5.4.

A cewar Bloomberg, kamfanin ya tafka asarar sakamakon karya darajar Naira da kuma shawarar babban bankin Nigeria na takaita sayar da dalar Amurka.

Sai dai kakakin kamfanin Tony Chiejina ya shaida wa BBC korar ma'aikatar ba shi da nasaba da batun tabarbarewar tattalin arziki da Nigeria ke fuskanta.