Wadanne irin Tukwane ne aka gano a Kano?
hako wasu manyan tukwanen kasa a unguwar Zangon Bare-bari a Kano
Bayan gano manyan tukwanen k'asa na tarihi a Kano a cikin makon jiya, wakilinmu Mukhtari Adamu Bawa ya zanta da Malam Nasir Sani Ahmad babban masanin kimiyyar al'umma da al'adunsu a Hukumar adana kayan tarihi ta Nijeriya da ke Kano, sai ku saurari hirar ta su a farkon wannan rahoton.
Tunda farko dai an hako wasu manyan tukwanen kasa a unguwar Zangon Bare-bari a karamar hukumar birni da ke tsakiyar birnin Kano.
Masu hasashe dai na cewa tukwanen ka iya kai wa shekaru 500 a duniya, ko da yake gwajin kimiyya ne kadai zai iya tabbatar da haka.
Tun bayan gano tukwanen ne a wani gida da ake sabunta ginawa, wasu da ba a san ko su wane ne ba suka haura da tsakar dare suka fasa daya daga cikin tukwanen da nufin kwashe abin da ke ciki.
Mai unguwar Zangon Bare-bari Malam Auwalu Rabi'u inda aka gano tukwanen, ya shaida wa BBC cewa tukwanen guda uku da ke cikin wani katon rami, manya-manya ne kamar girman mutum.
Ya ce bayan da aka gano su ne a ranar Alhamis aka shaida masa, inda shi kuma ya sanar da hukuma.
A makonnin baya ma, an gano irin wadannan tukwane a yankin Rangaza a karamar hukumar Nassarawa a birnin na Kano.
A shekara biyar zuwa shida da suka gabata ma a unguwar Agadasawa da ke birnin Kanon an taba samun tukunya daya , amma ba ta kai girman wadannan ba.
An hako manyan tukwanen kasan ne a unguwar Zangon Bare-bari a karamar hukumar Nassarawa dake tsakiyar birnin Kano