Sharhi: Shugaba Buhari, matar ka ta dace da zama a ko'ina

Shugaba Muhammadu Buhari da matarsa Aisha Buhari

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Shugaba Buhari ya mayar da martani ga matar sa a yayin wani taron manema labarai a kasar Jamus

Cikin jerin wasikun mu daga 'yan jarida a Afrika, wata marubuciyar Ghana, Elizabeth Ohene ta yi sharhi a kan kalaman Shugaba Muhammadu Buhari game da matarsa, Aisha Buhari.

Ta kuma bayyana inda take ganin shugaba Buhari ya yi kuskure.

Ta ce, ta je wani bikin aure a Washington DC a makon daya gabata, inda ta dauko batun saboda tunanin da ta ke yi game da rayuwar matan aure, musamman bayan kalaman da shugaba Buhari ya yi a kan matarsa.

A cewarta, shugaban ya yi katoɓarar da ba a taɓa ganin irinsa ba a bainar jama'a, inda ya ce "Aikin matata shi ne ta dafa min abinci, da kuma ta gyara min turaka."

Kalaman na nufin cewa bai kamata matar shugaban ta yi katsalandan a al'amuran da suka shafi siyasa ba, sai dai ta tsaya kawai wajen gudanar da ayyukan gida.

Maganganun siyasa ba a ɗakin girke-girke ake yin su ba, haka kuma ayyukan gudanar da mulkin kasa basu dace da falo ba, kazalika batutuwan zaɓe ba a uwar ɗaka ake tattauna su ba.

Ta ce tana sane da cewa kakakin shugaban kasar ya jaddada cewa cikin raha ne shugaban ya faɗi maganar, kuma bai kamata a ɗauki zafi a kan zancen ba.

To amma a ina ya kamata a tattauna batun bikin aure ko kuma a ina ma za a gudanar da bikin shi kansa? A dakin girke girke ko kuma falo ko kuma uwar ɗaka?

A bar zancen maza

A Ghana, aure shi ne haɗuwar iyalai biyu, ba wai ma'auratan su biyu kaɗai ba.

A bikin da ta je a Washington DC da ke Amurka, Naabia ce amaryar kuma 'yar uwarta ce, inda iyayenta ma 'yan asalin kasar Ghana ne, amma kuma gaba ɗaya rayuwarta a ta yi ne a Amurka.

Ango kuma shi ne John, haifaffen jihar Texas ne a Amurka, amma kuma yana da dangi a kasashen Italiya da Scotland da yankin Wales.

'Yar jaridar ta ce a yayin bikin sai ta gano cewa iyayen ango basu damu da cewa iyalai biyu ne zasu haɗe ba, kamar yadda ta yi zato.

Amma kuma mahaifin John bai ji daɗin yadda al'adar Ghana ta hana maza halartar biki ba, face shi angon shi kaɗai.

Gaba ɗaya mata ne ke gudanar da ayyukan ɗaurin aure, a al'adar Ghana, sai dai maza su zauna gefe guda su sanya musu ido.

Asalin hoton, Elizabeth Ohene

Bayanan hoto,

Abubuwan da matar Aisha Buhari ta fadi a hirarta da BBC 'yan Najeriya da dama sun sha fadin irinsu, kuma babu shakka shugaba Buhari ya ji

Bayan an kammala bikin ne Elizabeth ta yi wa mahaifin John alkawarin cewa za ta jagoranci wata fafutukar ganin an daina ware maza daga harkokin bukukuwa a Ghana.

Lamuran da suka afku a makon da ya gabata, sun sa na mayar da hankali na kacokam kan wasu fitattun mata biyu.

Da matar shugaban Amurka, Michelle Obama, da kuma matar shugaban Najeriya Aisha Buhari, cikin 'yan sa'o'i ƙalilan kowacce ta yi fice a jaridun duniya ta hanyoyi daban-daban.

Abubuwan da Aisha Buhari ta faɗi a hirarta da sashen Hausa na BBC, 'yan Najeriya da dama sun sha faɗin su, kuma babu shakka shugaba Buhari ya ji.

Amma kuma ya san da cewa fitowar kalaman daga bakin matarsa zai basu muhimmanci sosai.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Misis Obama ta soki Donald Trump kan yadda ya ke wulakanta mata

Misis Obama kuma tana bayani daga a ɗakin dafa abinci zuwa falo, da kuma daga kan tituna, tana bayani a yayin tafiye-tafiyen tawagar kamfen 'yan siyasa, haka kuma tana bayani daga uwar ɗakinta.

Saboda haka, shugaba Buhari, bama kunyar faɗin ɗakin kwanciya.

Misis Obama tana bayani daga kowanne ɗaki, kuma duk kalamanta na da muhimmanci don haka ake sauraronta.

Aisha Buhari, kamar ita Michelle Obama, tana jawabi daga kofar ɗakin ta ne kuma mun ji ta.

Ina gani zan ci gaba da bayar da goyon baya ga tsarin da ya bar ɗaurin aure ga mata kawai.

Domin ya jaddada cewa matar aure ta dace da zama a gaba -gaba cikin harkokin gida.