EFCC ta damke Bala Mohammed da Reuben Abati

Shugaban EFCC Ibrahim Magu
Bayanan hoto,

Shugaban EFCC Ibrahim Magu ya ce ba sa nuna bambancin siyasa a aikinsu

Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta'annati, EFCC ta kama tsohon ministan Abuja, Sanata Bala Mohammed.

Hukumar ta EFCC ta kuma kama kakakin tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan, Dokta Reuben Abati a ranar Litinin din nan.

Wata majiya mai karfi ta hukumar ta EFCC ta tabbatar wa da BBC cewa lalle tsoffin jami'an tsohuwar gwamnatin biyu suna hannunta.

Sai dai kuma majiyar ba ta yi wa BBC karin bayani kan dalilin kama mutanen biyu ba, da kuma lokacin da za ta gabatar da su a gaban kotu.

'Yan hamayya da masu sukan lamirin hukumar ta EFCC, na zarginta da kama jami'an tsohuwar gwamnatin Goodluck Jonathan ne kawai.