Mahara sun kashe 'yan sanda da yawa a Pakistan

Wasu da harin ya rutsa da su

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Sama da mutane 100 sun jikkata a harin, wasu raunin ya yi tsanani

Wasu 'yan bindiga sun kai hari makarantar horas da 'yan sanda da ke Quetta, a Pakistan, tare da hallaka 'yan sandan da ke samun horo kusan 60 da jikkata wasu da dama.

Wakilin BBC ya ce sojoji sun sanar da cewa da tsakar dare ne, kusan maharan uku zuwa shida daga ciki 'yan kunar-bakin-wake, suka afka wa barikin, mai nisan kilomita 15 daga birnin Quetta.

Jami'an tsaro sun yi saurin kai dauki, inda su kai ta harbe-harbe har suka hallaka wasu maharan, yayin da sauran su ka yi saurin sanya riguna masu bama-bamai a jikinsu suka yi kunar-bakin-wake.

Kawo yanzu babu wanda ya dauki alhakin kai harin, amma wani babban jami'in tsaro ya shaida wa BBC cewa ya yi amanna da cewa an turo maharan ne daga makociyarsu Afghanistan.