Kenya: Kungiyar Al-Shabab ta kashe mutum 12

Gidan da Al-shabab ta kai hari
Bayanan hoto,

Mutanen da aka kashe na zama ne a wannan gida

A kalla mutane 12 ne suka rasa rayukansu a wani hari da kunguyar al-Shabab ta kai a kasar Kenya.

'Yan sanda da ke kan iyakar garin Mandera sun ce ana kyautata zaton maharan sun yi amfani da bama-bamai a harin da suka shafe tsawon dare suna kai wa.

Sun kai harin ne kan wani gidan saukar baki da ke Arewa maso Gabashin garin.

Harin dai shi ne mafi muni a hare-hare na baya-bayan nan a kan Kiristoci da ke lardin da Musulumai suka fi yawa.

Kafafen yada labarai na al-Shabab sun ce harin ya kashe Kiristoci wadanda ba mazauna yankin ba.

Jaridar Daily Nation ta ce a cikin wadanda suka rasa rayukansu har da wasu mutane wadanda suka je Mandera domin gabatar da wasu litattafai a makarantu.