Shekarar 2016 ce mafi muni ga 'yan gudun hijira - MDD

Jirgin ruwa da ke dauke da 'yan gudun hijira

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Masu safara jama'a na cunkusa dubban mutane a cikin jiragen ruwa marasa kyau a lokaci guda dagangan

Hukumar da ke kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce shekarar 2016 ce mafi muni ga 'yan gudun hijira da 'yan cirani wadanda ke ketare kogin Bahar-rum.

Alkaluman da hukumar ta fitar sun nuna cewa har zuwa 23 ga watan Oktoba, an rasa rayuka 3,740.

Da kadan ne alkaluma 3, 771 na shekarar 2015 suka haura na bana, a cewar hukumar.

Hukumar ta kara da cewa watanni biyu masu tattare da hadari mafi muni na tsallaka tekun na nan tafe.

Abin da majalisar da kuma kungiyar kula da 'yan cirani ta duniya suka fi damuwa a kai shi ne, yayin da aka samu raguwar adadin mutanen da ke tsallakawa sama da miliyan a bara, idan aka kwatanta da kusan 300,000 na bana, yawan mace-mace ya karu.

Majalisar Dinkin Duniya ta danganta karin da ake samu da abubuwa da dama da suka hada da:

  • Amfani da hanyoyi masu hadari
  • Tsallaka kogi a yanayi mara kyau
  • Cunkusa dubban mutane a cikin jiragen ruwa kanana a lokaci guda

Mahukunta sun ce hakan na kara takura masu aikin ceto da tilast musu bullo da sabbin dabaru.