Burtaniya za ta fadada fillin jiragen saman Heathrow

Filin jingin Heathrow dake Burtaniya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Wasu 'yan majalisar dokoki masu adawa sun soki shawarar

Gwamnatin Burtaniya ta amince ta fadada filin tashi da saukar jiragen sama na Heathrow domin bunkasa tattalin arzikin kasar.

A ranar Talata ne dai ministoci suka amince da shawarar a wurin wani taron kwamitin majalisar zartarwa na kasar.

Sakataren Sufuri, Chris Grayling ya kira shawarar da aka yanke da "mai muhimmanci" kuma ya kara da cewa fadadawar za ta inganta sadarwa tsakanin Birtaniya da ragowar kasashen duniya da bunkasa cinikayyada da ayyukan yi.

Sakataren zai kuma zai yi jawabi a majalisar dokokin kasar domin fayyece matakin da gwamnatin ta dauka.

Fadada filin jirage a kudu maso gabshin Ingila wani abu ne da aka dade ana jan-in-ja a kai a cikin shekaru da dama.

Filin jirgin sama na Heathrow ya yi fice a duniya kuma yana da muhimmanci ta fuskar kasuwanni.

Sai dai matakin fadada shi ya jawo hankulan 'yan majilasar dokoki masu adawa da dama wadanda mazabarsu ke kusa da shi.