Natasha Annie Tonthola: "Yakin da na yi da masu lalata da mata a Malawi'"

Natasha Annie Tonthola

Asalin hoton, ELDSON CHAGARA

Bayanan hoto,

Yakin da Natasha Annie Tonthola ke yi da al'adar 'kura' a Malawi

A watan Yuli ne BBC ta bayar da labarain wani mutum dan kasar Malawi, wanda ake biya domin ya yi lalata da 'yan mata da suka fara al'ada, a kauyensa.

An dai kama shi kuma yana fuskantar shari'a a yanzu, duk da cewar al'adar 'kuraye' wato sunan da ake kiran maza irinsa da ake biya su yi irin wannan aiki- ta zama ruwan dare a wannan yankin.

Daga baya kuma wata mata 'yar Malawi mai suna Natasha Annie Tonthola, ta nemi BBC domin ta shaida mana yadda ta tsinci kanta a hannun wani 'kure' lamarin da ya ingiza ta wajen fafutukar neman kariya ga mata da 'yan mata da ke fuskantar wannan al'ada.

Ga kuma labarin nata

Ta ce, ''ni ce babba cikin mu biyar wajen iyayena, kuma na girma ne a wani kauye da ke tsakiyar wata gunduma da ke kusa da Lilongwe babban birnin Malawi, ina kuma da shekaru 13 lokacin da lamarin ya afku.

Mahaifina ya fito ne daga wani kauye da ke kusa da Mulange, a kudancin kasar, kuma bayan da na soma al'adata ta farko ne aka aika ni wajen bikin al'adar, wanda kuma ba ka da ta cewa dole ka je tun da duk wata 'ya mace a kauyen sai ta yi.

An ce mana ne za mu je mu koyi yadda ake zama mace, kuma ka zama mai rike gaskiya, don haka nake ta azarbabin zuwa, kamar kowacce yarinya.

A rana ta karshe daya daga cikin tsofaffin matan suka ce da mu mun kawo rukuni na karshe a bikin al'adar, ta ce wani kura zai zo ya kawo mana ziyara. Ta ce "amma kar ku damu, ba kura, dabbar daji nake nufi ba, ina nufin wani mutum ne."

Amma ba mu san ko wanene 'kuren' ba, da kuma ko abin da zai yi mana.

Ba sa gaya mana cewa zai kwana da mu ne.

Kowacce cikinmu na rike da kyalle da aka ba mu mu shimfida a kasa.

Bayanan hoto,

Taswirar kasar Malawi da ke nuna kauyen Natasha

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

An shaida mana cewa, lokaci ya zo da za mu nuna cewa mun iya kula da miji, kuma mun san yadda za mu kula da mazajenmu nan gaba.

Sai kuma a rufe mana idanu da dan kyalle.

Bai kamata ka nuna kana jin tsoro ba, ko ka san abin da ke faruwa.

Mutum zai shigo ne ya umurce ka da ka bude kafafunka ya yi abin da zai yi.

Ba a ma gaya mana ko wanene, manyan ne kadai suka san shi.

Muna yara ne, saboda haka duk ba mu saki jiki ba, don haka sai ya bude kafafunmu da karfi.

Gaskiya na ji zafi sosai, kuma na yi murna sosai bayan da ya gama.

Daga nan, sai babbar jagorar tsoffin matan ta shigo ta ce, "Ina taya ki murna, yau kin zama mace."

Mata da dama ba su mayar da shi komai ba saboda an sauya musu tunaninsu, gani muke ba komai ba ne tun da al'ada ce.

Amma kuma 'kuren' ba ya amfani da kariya, don haka 'yan mata da yawa sukan yi ciki.

Da muka koma gida an hana mu mu'amala da sauran 'yan matan da ba su riga sun yi bikin al'adar ba.

An hana ni gaya wa kanwata abin da ya faru.

Yanzu kuma yara mata na kawo jiki da wuri, tun da wasu ma a shekara 10 ko 11 suke ganin jinin al'adarsu.

Bayan bikin al'adar, rayuwata ta sauya baki daya.

Mahaifina wanda dan sanda ne ya rasu a wannan shekarar.

Ga al'ada mace tana cikin gado, don haka idan mai gida ya rasu sai kaninsa ya gaje ta, domin ya ci gaba da kula da iyalan da aka bari, amma mahaifiyata ta ki amincewa da hakan.

Maimakon haka sai muka koma Afrika Ta Kudu, domin ita mahaifiyata tana da dangantaka da kasar, saboda haka da kawuna ya gayyace mu sai muka koma can muka soma wata sabuwar rayuwa.

Mun nemi aiki muka fara, ni dai sai da na kara shekaru na samu ayyuka a gidajen sayar da abinci da kuma wuraren gyaran gashi.

Akwai kuma lokacin da na zama 'yar aikin gida.

Duk da cewa na yi aiki sosai, ba mu samu isasshen kudin kula da kanmu ba ballantana shiga makaranta.

Sai wasu 'yan uwana kuma a can Malawi suka shaida min cewa akwai wani mutum da ya ce zai biya mini kudin makaranta idan har na amince zan aure shi.

Na kusa kaiwa shekara 16 a lokacin, kuma ban so yin aure da wuri haka ba.

Mahaifiyata ita ma ba ta yarda ba.

Amma kuma ina matukar bukatar kammala karatuna, ga shi ayyukan da mahaifiyata ke ta yi sun soma shafar lafiyata.

Saboda haka na ce na amince, kuma sai dukkanmu muka shirya muka koma Malawi.

Muka yi aure kamar yadda al'ada ta tanadar, ya kuma cigaba da biya min kudin makaranta, da kuma kula da 'yan uwana baki daya.

Maigidan nawa ya girme ni da shekara 15, yana da ilimi kuma ga shi dan kasuwa ne, amma kuma yana duka na.

A kodayaushe sai ya buge ni, kuma har yanzu ina da tabo iri-iri na dukan da yake min.

Na dauki ciki lokacin da nake da shekara 17, amma kuma na yi sa'ar kammala jarrabawata kafin na haifi 'ya mace.

Dukan da mijin nawa ke min ya yi tsananin har sai da na kusa barin cikin, ga shi kuma mutum ne mai neman mata a waje sosai.

Raina yana matukar baci da lamarin, saboda ba haka na so ba a rayuwata.

Na san kuma yana yin hakan ne domin ya san babu yadda zan yi, ba ni kuma da inda zan je.

A nan ne kawuna da ke Afrika Ta Kudu ya sake kawo mi taimako.

Yana sane da cewa ina da sha'awar ayyukan kayan kawa, don haka ya tallafa min na shiga makarantar dinki.

Mijina ya ce min idan har na rabu da shi, to sai ya neme ni duk inda nake ya kashe ni.

Don haka na ce masa zan yi tafiya ne in dawo nan da mako daya ko biyu.

Amma ban sake komawa ba, maimakon haka ma sai na shiga makaranta, kuma na cigaba da ciyar da kaina ta hanyar aiki da wani gidan sayar da abinci.

Daga baya dai sai na koma Malawi na fara aikin dinki, inda na ke yi wa manyan mutane dinki a kasar.

Na kuma bude gidan sayar da abinci, saboda ina matukar son harkar dafa abinci.

Kazalika na kirkiro wata kungiya da ke fafutuka kan abubuwa da dama, kamar tabbatar da yara mata sun cigaba da karatu da yaki da auren wuri da kuma fadakar da mutane kan wasu dabi'u na al'ada.

Kamar al'adar 'kura' da ke barazana ga rayuwar yara mata. da kuma ilmantar da su kan cutar AIDS ko SIDA, ko kuma Kanjamau, da yin ciki a waje da kuma fadakarwa kan ilimin mahaifar mace.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Idan budurwa ta kawo jiki ta soma ganin jinin al'ada sai a kai ta wajen 'kura' domin ta koyi iya kwanciya

Duk da haka dai matsalolina da mijina ba su kare ba, saboda, da ya ji cewa na komo Malawi, sai ya soma bibiyata, yana cewa "Idan ba ki dawo wurina ba, ba zan bari ki auri kowa ba."

Wata rana sai ya zo gidan da nake zama, ban kuma san yadda ya gano shi ba, to amma da yake na gan shi cikin nutsuwa sai na bar shi ya shigo.

Ya ce yana bukatar ganina ne, kuma ya ga 'yarsa, wacce ta kai shekara uku a wannan lokacin.

Ya ce min shi har yanzu yana kaunata, kuma na yi masa gafara domin ya sauya rayuwarsa yanzu.

Ya ce, "Har yanzu akwai aure tsakaninmu, na kuma yi miki komai a rayuwa"

"Ba don ni da na biya miki kudin makaranta kuma na yi ta kula da 'yanu wanki ba, da ba ki kawo haka ba a yau. Don haka dole ki saka min."

Na ce masa ta faru ta kare tsakanina da kai, domin gaskiya ba ni da niyyar komawa wurinsa.

A nan ya yi ta yi min kururuwa har ya soma tarwatsa min abubuwa, kuma ya shake min wuya, duk da cewa 'yarmu tana zaune kan cinyata.

Da tuni ya kashe ni, ba don makota da suka ji ihuna suka shigo suka cece ni ba.

Nan da nan suka shigo suka fitar da shi da karfi.

Ban so na kai shi kara kotu ba domin bana so zancen ya bazu a gari, amma na dole na yi hakan domin, na samu kariya daga gare shi, domin kada ya sake kusanta ta.

Asalin hoton, ELDSON CHAGARA

Bayanan hoto,

Natasha ce ta kafa wata gidauniya mai suna, Mama Africa Foundation Trust

Wannan abu ya yi matukar kada ni, kuma na san da cewa irin haka na faruwa da manya da 'yan mata da dama.

Kungiyata dai ta cigaba da fadakar da mutane, amma kuma mun fuskanci kalubale da yawa, musamman game da zancen al'adar 'kura' da kuma wacce ta shafi gadon macce bayan mijinta ya rasu.

A wasu yankuna da muka kai wa ziyara, har ce mana suke, "don kuna da ilimin boko, ba shi ya ba ku hurumin ku gaya mana yadda za mu tafiyar da rayuwarmu ba. Wadannan al'adu sun dade tun kaka da kakanni, mun kuma dade muna yinsu, ba tare da wata matsala ba."

Amma kuma mun samu wasu manya da suka saurare mu, kuma suka daina wasu al'adun a kauyukansu.

Cikin ayyukan nawa na gano cewa akwai rashin daidaito wajen ilimin mata, inda wasu iyayen idan suka shiga wani matsanancin hali na rashin kudi, sai su cigaba da biya wa 'ya'yansu maza kudin makaranta su bar 'ya 'ya mata.

Idan har yarinyar ta bar makarantar kuma sai a yi maza a yi mata aure, wai domin kada ta zauna a gida haka kawai.

Kazalika, mata da dama ba sa zuwa makaranta lokacin da suke jinin al'ada saboda ba su da kudin sayen audugar al'ada.

To domin tunkarar wadannan matsalolin, daya daga cikin abubuwan da kungiyar tawa ke yi, shi ne ta rarraba wa mata audugar haila.

Muna hada su ne jaka guda, tare da bante, da dai wasu abubuwa da za su bukata.

Dukkansu kuma ana hada su ne da abubuwan da ba za su yi wahalar zagwanyewa ba a kasa, marassa tsada kuma masu karko, har su kai shekara biyar.

Muna kuma ilmantar da su da ba su kwarin gwiwa wajen takaita zubar da shara, da kuma tsaftace muhalli.

A shekarar 2011, na gano cewa dole ne mu kafa wata kwakkwarar kungiya a hukumance, daga nan ne kuma muka kafa wata gidauniya mai suna Mama Africa Foundation Trust.

A wannan kungiya mun rabar da audugar al'ada ta mata, wadda ba mu san yawanta ba, na kuma sanya wa wannan shirin suna Project Dignity.

Duk da abubuwan da suka faru, ina da kwarin gwiwa sosai a kan abin da gobe za ta haifar.

Ina gani akwai mata da yara da dama da suka fuskanci matsalar al'adar 'kura', da cin zarafi da kuma duk wani kalubale a yankunansu.

Akwai kalubale a gabanmu, amma ina da kaykkyawan fata ga abin da gobe za ta haifar.