An zargi wata nos da kisan tsofaffi 8 da take kula da su a Kanada

Ma'aikaciyar jiyya, Ms Wettlaufer

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Matar ta rika bayyana irin faman da take yi da matsalar shan barasa a shafinta na Facebook

An tuhumi wata ma'aikaciyar jiyya ko 'nus' da laifin kashe wasu tsofaffi marassa lafiya da take kula da su a wasu gidajen kula da tsofaffi a lardin Ontario na kasar Kanada.

'Yan sanda sun ce ma'aikaciyar jiyyar mai shekara 49, mai suna Elizabeth Wettlaufer, ta hallaka mata biyar da maza uku da ke karkashin kulawarta a gidajen kula da tsofaffi biyu.

Jami'an tsaron sun ce sun fara gudanar da bincike ne a kan lamarin bayan da aka tsegunta musu maganar.

Haka kuma sun kara da cewa, tsofaffin da nos din ta kashe, wadanda shekarunsu sun kama ne daga 75 zuwa 96, an ba su wasu magunguna da ba a fayyace wadanne iri ba ne.