Gambia za ta fice daga Kotun Duniya

Asalin hoton, AFP
Shugaba Jammeh kan jawo ce-ce-ku-ce a duniya, ko a 2007 ya ce zai iya magance cutar AIDS ko SIDA da maganin gargajiya
Gwamnatin Gambia ta zargi kotun hukunta manyan laifuka ta duniya, da nuna bambanci launin fata a ayyukanta musamman a kan 'yan Afurka, dan haka ba tare da bata lokaci ba Kasar za ta fice daga kotun.
Kasar ta yammacin Afurka ta dauki wannan mataki ne bayan kasashen Afurka ta Kudu da Burundi su ma sun dauki matakin ficewa daga ICC din.
Shugaba Yahya Jammeh shi ke jagorancin Gambia tun da ya dare karagar mulki a shekarar 1994 bayan juyin mulkin da ya yi.
Jammeh ya kawar da jagoran kasar na farko, Sir Dawda Kairaba Jawara, wanda ya fara mulki a matsayin Fraiminista daga 1962 zuwa 1970, sannan kuma ya zama shugaban kasa daga 1970 zuwa 1994.
A watan Disamba mai zuwa ne ake sa ran za a gudanar da babban zabe a kasar, kuma a farkon shekarar nan aka cafke jagoran 'yan hamayya Ousainou Darbo da wasu mutane 18.
An kuma yanke musu hukuncin zaman gidan yari na shekara uku bisa samunsu da hannu a shirya zanga-zangar da hukumomin kasar suka haramta.
Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International, ta kira hukuncin alamun cigaba da take hakkin dan adam da ake yi a Gambia.