Dan Amurka ya lashe gasar Man Booker Prize a karon farko

Paul Beatty tare da Duchess ta Cornwall

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto,

Paul Beatty tare da Duchess ta Cornwall

Paul Beatty ya zama dan kasar Amurka na farko da ya lashe gasar kagaggun labarai ta Man Booker Prize da littafin da ya rubuta mai suna The Sellout inda ya yi shagube ga masu nuna wariyar launin fata.

An gina littafin ne kan labarin wani yaro bakar-fata wanda ya yi kokari ya dawo da bauta da kuma yin iyaka tsakanin farar-gata da bakar-fata a wani yankin marasa galihu da ke birnin Los Angeles.

Shugabar alkalan gasar, Amanda Foreman, ta ce littafin ya bankado abubuwan da ake kyama a cikin al'uma.

An sanar da wanda ya lashe gasar ne a wurin wani biki na birnin London ranar Talata.

Paul Beatty, wanda ya karbi kyautar £50,000 daga wajen Duchess ta Cornwall, ya yi matukar mamakin yadda ya lashe gasar, inda ya rude har ta kai ga ya kusa kasa cewa komai.

A cewarsa,"Na tsani yin rubuce-rubuce. Wannan littafi ne wanda ya yi matukar wahalar rubutawa. Na sani karatu na da matukar wuya."