Kompany ya ce ya gaji da wasa — Guardiola

Kompany ya shafe sama da shekara takwas a City

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Kompany ya shafe sama da shekara takwas a City

Kyaftin din Manchester City Vincent Kompany ya nemi a sauya shi daga wasan da Manchester United ta doke su da ci 1-0 idan an tafi hutun rabin lokacin saboda ya "gaji."

Dan wasan, mai shekara 30, ya buga wasansa na biyu a kakar wasa ta bana ne a karawar da suka yi da United bayan ya yi jinya a watan Satumba.

Kocin City Pep Guardiola ya ce Kompany "ya gaya mana cewa ya gaji, kuma ba zai iya buga wasan ba bayan hutun rabin lokaci

City dai ba ta yi nasara ko sau daya ba a wasanni shida da suka buga.

Guardiola ya kara da cewa abu mafi muhimmanci a game da Kompany shi ne "bai ji rauni ba."

Kompany, wanda ke fama da ciwon sha-raba, ya cew zai gaya wa likotoci gaskiya halin da yake ciki na rashin lafiya.

Dan wasan na kasar Belgium ya buga wa City da kasarsa wasa 25 a kakar wasan bara, wato ya ragu daga wasa 38 a kakar wasan da ta gabaci ta a bara da kuma ledar da ya murza sau 40 a kasar wasa ta shekarar 2013-14.