Jirgin kasan Kamaru ya zarta ka'idar gudu a lokacin da ya yi hadari

Jirgin da ya yi hadari a Kamaru

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Wasu daga cikin taragwan jirigin kasan sun jirkice

Wani babban jami'i a kamfannin jiragen kasa na Faransa ya ce jirgin kasan nan da ya yi hadari a ranar Juma'ar makon da ya gabata, ya zarta ka'idar gudu da ya kamata a ce yana yi.

Hadarin dai ya yi sanadiyar mutuwar mutane 79 kuma ya jikkata wasu mutane 600.

Da farko dai an dora alhakin hadarin a kan cunkuson mutanen da ke cikin jirigin.

Sai dai kamfanin jirgin kasa na Bollore ya ce jirigin kasa ya zarta ka'idar gudu wani wuri da ya kamata a ce ya rage gudun da yake yi.

Jirgin dai na hanyarsa ta zuwa Doula daga babban birnin kasar, Yaounde a lokacin da taragwan suka jirkice.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Mutanen da suka tsira da ransu suna barin wurin da hadarin ya auku

Eric Melet, shugabana kamfanin Bollore reshen Afirka, ya shaida wa BBC cewa bai kamata a ce jirgin ya doshi inda ya yi hadarin ba tare da ya rage gudun da yake yi ba.

Mr Melet ya ce a lokacin da jirgin ya doso inda hadarin ya auku, yana gudu fiye da ka'idar gudun da ya kamata ace yana yi a lokacin.