Mata sun fi maza aikatuwa a duniya

Mata da maza game da tattalin arki

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Gibi game da tattalin arziki ya fi yawa a yanzu tun a shekarar 2008.

Majalisar tattalin arziki ta duniya ta ce a yawancin lokuta mata na yin aiki fiye da maza.

A akasarin lokuta, a yini, mata suna yin aikin minti 50 sama da maza, kamar yadda bayanai a wani rahoto da bangaren majalisar da ke kula da gibin da ke tsakanin mata na duniya ya nuna.

Rahoton ya ce yawan aikin da mata ke yi ba tare da ana biyansu ba, na kara wa mata dawainiya, kuma ya bayyana cewa, fifikon da ake bai wa maza a kan mata game da tattalin arziki, ba zai kare ba har sai a kalla zuwa shekara 170.

A cewar Majalisar tattalin arziki ta duniyar, gibin da ake samu a yanzu ya fi fadi fiye da kowane lokaci, tun daga 2008.

Rahoton ya kuma ce kusan kashi daya cikin hudu na mata biliyan suna neman aikin yi a duniya a shekara goma da suka gabata.

Duk da dai maza suna da kashi 34 cikin 100 na aikin da ake biya fiye da mata, mata suna amfani da akasarin lokacinsu a aikin da ba a biya, kamar ayyukan gida, da kula da yara, da kuma kula da mutane wadanda suka manyanta.